Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa, kungiyar gwagwarmayar muslunci ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakkausar da yin Allawadai da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da sojojin mamayar Amurka suka yi a kasar Afghanistan tare da kone shi domin tsokanar musulmi.
A kalla mutanen 10 ne suka rasa rayukansu a kasar Afganistan a ci gaba da zanga zangar nuna fushi kwanaki ukku a jere wanda mutanen kasar daga bangarorin daban daban suke yi don keta hurumin Al-Qur'ani mai girma wanda sojojin mamaya suka yi a barikin Bagram a ranar litin da ta gabata.
Akalla mutum guda ne ya rasa ransa a yau Alhamis sannan wasu 4 kuma suka ji rauni, biyu daga cikinsu yansanda ne, a lardin Baglan.
Yau ne kwana ta ukku a jere wanda yansanda kasar Afganistan suke kokarin dakatar da zanga zangar nuna fushi wanda mutanen kasar ta Afagnistan suke yi kan kona al-kur'ani mai girma wanda sojojin mamaya suka yi.
A ranar litinin da ta gabata ce wasu sojojin mamaya da ke Sansanin sojojin NATO a Bagram suka kona wasu littafan addini daga cikinsu har da wasu kofi kofi na Al-Qur'ani mai girma.
A zanga zangar jiya laraba dai mutane kimani 9 suka rasa rayukansu a yankunan daban daban da kasar ta Afganistan kan wannan lamarin.
958164