Bangaren kasa da kasa: a jiya ne biyar ga watan isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya musulmi a kasar Malaishiya suka gudanar da wata gagaramar zanga zangar yin Allah wadai a gaban ofishin jakadancin Ameriuka a Kalalanpur fadar mulkin kasar domin nuna adawarsu da yadda wasu sojojin mamaye na Amerika a kasar Afganistan suka kona kur'ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a jiya ne biyar ga watan isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya musulmi a kasar Malaishiya suka gudanar da wata gagaramar zanga zangar yin Allah wadai a gaban ofishin jakadancin Ameriuka a Kalalanpur fadar mulkin kasar domin nuna adawarsu da yadda wasu sojojin mamaye na Amerika a kasar Afganistan suka kona kur'ani mai tsarki. Wannan zanga zanaga kungiyar addinin musulunci PAS a kasar ta Malaishiya ta shirya ta hanyar gayyatar musulmin kasar das u taru a gaban ofishin jakadancin Amerika a wannan kasa bayan gudanar da sallar juma'a domin gudanar da zanga zanagar yin Allah wadai da wannan mummunan aiki da takalar fada na sojojin mamaye na Amerika a kasar Afganista da suka kona kur'anai masu tsarki .Kuma a wannan zanga zanagar dubban musulmi ne suka samo halarta tare da rera take iri iri kamar dole a girmama kur'ani kuma la'antar Allah ta tabbata kan sojojin Amerika da Allah sinewa sojojin Amerika. A kasashe da daman a musulmi an gudanar da irin wannan zanga-zanga ta yin Allah wadai da sojojin Amerika da suka kona kur'anai a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan.
959587