IQNA

Musulmi Pakistan Suka Gudanar Da Zanga Zanagar Allah Wadai Da sojojin Amerika

19:00 - February 26, 2012
Lambar Labari: 2281210
Bangaren kasa: musulmi a kasar Pakistan a ranar biyar ga watan isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya bayan kammala sallar juma'a sun gudanar da wata gagaramar zanga-zanaga ta yin Allah wadai datofin Allah tsine kan Amerika a kokarinsu na nuna babbar adawarsu da cin mutuncin kur'ani mai girma da wasu sojojin mamaye na Amerika suka yi a kasar Afganistan na kona Kur'anai.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: musulmi a kasar Pakistan a ranar biyar ga watan isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya bayan kammala sallar juma'a sun gudanar da wata gagaramar zanga-zanaga ta yin Allah wadai datofin Allah tsine kan Amerika a kokarinsu na nuna babbar adawarsu da cin mutuncin kur'ani mai girma da wasu sojojin mamaye na Amerika suka yi a kasar Afganistan na kona Kur'anai. Musulmin da suka gudanar da wannan gagaramar zanga-zanga ta ranar juma'a sun taru ne a tsakiyar birnin Lahur a lardin Panjab na kasar ta Pakistan inda suka bayyana adawarsu a fili da duk wani mataki na cin fuska da cin mutunci kur'ani mai tsarki musamman wannan mataki da kona kur'ani mai tsarki da wasu sojojin Amerika suka yi a kasar Afganistan.Wannan jerin gwano da zanga zanaga kungiyar Jama'atul islami da kungiyar jama'atul Da'awa a Pakistan suka gudanar kuma an samu halartar musulmi masu yawan gaske da suka yi ta rera taken yin Allah wadai da Amerika da mutuwa kan amerika kuma suka bukaci musulmin duniya da su hada kansu na tunkarar makiyansu a ko ina suke a fadin duniya.

959503

captcha