IQNA

Katar Ce Ke Daukan Shirya Makarkashiyar Haddasa Rikici A Suriya Ta fakewa Da Addini

13:30 - February 27, 2012
Lambar Labari: 2281724
Bangaren kasa da kasa: a lokacin da aka kirkiro da kungiyar hadin kan malaman addinin musulunci a shekara ta dubu biyu da hudu karkashin kulawa ta musamman ta sarkin kasar Katar da ayyana Sheik Yusuf Kardawi a matasayin shugaban wannan kungiyar babu wanda zai yi zaton wannan babbar kungiya zata rikide ta zama ta cimma burin siyasa a yankin da kuma a kasa da kasa ta kuma zama makamin siyasa na Katar.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a lokacin da aka kirkiro da kungiyar hadin kan malaman addinin musulunci a shekara ta dubu biyu da hudu karkashin kulawa ta musamman ta sarkin kasar Katar da ayyana Sheik Yusuf Kardawi a matasayin shugaban wannan kungiyar babu wanda zai yi zaton wannan babbar kungiya zata rikide ta zama ta cimma burin siyasa a yankin da kuma a kasa da kasa ta kuma zama makamin siyasa na Katar. Sheik Yusuf Kardawi limamin juma'ar birnin Doha babban birnin kasar katar da ke samin goyan baya da taimakon makudan kudade daga mahukumtan kasar Katar da gidan sarautar wannan kasa a yan shekarun nan na bayan bayan ya samu jan hankalin daruruwan malamai da masu bincike na musulmi a kasashen larabawa da na musulmi da ma nahiyar Turai da arewacin amerika amma a maimakon ya hada kawunan musulmi da samar da wani yanayi na hadin kai a tsakanin musulmi da kuma kokartawa wajan magance matsalolin da musulmi ke fuskanta a kasashe daban daban na duniya ana amfani da wannan kungiya ta hadin malamai musulmi na duniya wajan haddasa rikici da sabani a tsakanin musulmi.


959878
captcha