Bangaren kasa da kasa, kona alkur'ani mai tsarki da sojojin mamayar Amurka suka yi a kasar Afganistan tamkar shelanta wani yaki ne da Allah madaukakin sarki domin kuwa ba wai wulakanci ne kawai ga mabiya addinin muslunci, tozarci ne ga dukaknin hallitun ubangiji baki daya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da daya daga cikin maman kur'ani na kasar Masar Farjallah Shazili ya bayyana cewa, abin da ya faru na kona alkur'ani mai tsarki da sojojin mamayar Amurka suka yi a kasar Afganistan tamkar shelanta wani yaki ne da Allah madaukakin sarki domin kuwa ba wai wulakanci ne kawai ga mabiya addinin muslunci, tozarci ne ga dukaknin hallitun ubangiji baki daya, domin kuwa littafinsa ne da ke dauke da kalamansa masu tsarki.
Mutanen 6 ne suka rasa rayukansu a ci gaba da zanga zangar da mutanen kasar Afganistan suke yi kan keta hurumin Alkur'ani mai girma wanda sojojin Amurka suka yi a ranar litinin da ta gabata.
A jihar Kandus na arewacin kasar an bada rahoton mutuwar mutane 3 a lokacinda wasu masu zanga zanga suka yi kokarin shiga wani ofishin MDD da ke jihar.
Majiyar ma'aikatar cikin gida na kasar Afganistan ta bayyana cewa an kashe jami'an sojojin kasashen waje guda biyu a ma'aikatar a yau asabar. Wannan kuma ya sanya babban komandan sojojin NATO a kasar na Afganistan ya bukaci sauran sojojin kasashen waje da suke aiki a wasu ma'aikatun kasar da su dawo barikokinsu don kare lafiyarsu.
Yau ce kwana ta 5 a jere wanda munane a kasar Afganistan suke zanga zangar yin Allah wadai da sojojin mamaya wadanda suka kona alkur'anai a sansanin sojojin su dake Bagram a ranar Litinin da ta gabata. Shugaba Obama na kasar Amurka ya nemi uzuri kan keta hurumin lakur'ani mai girma wanda sojojin NATO suka yi a kasar ta Afganistan, amma mutanen kasar suna bukatar a kama kuma a hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.
960731