Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, Sheikh Muhammad Zagmut wani babban malamin addinin muslunci a kasar Lebanon ya yi kakkausar ga gwamnatocin kasashen larabawa hard a na musulmi kan rashin tabuka komai dangane da kona kur'ani mai tsarki da sojojin Amurka suka yi a kasar Afghanistan a cikin makon da ya gabata.
Akalla mutane tara ne su ka rasa rayukansu a ci gaba da zanga-zangar da mutanen Afghanistan su ke yi na yin Allah wadai da kona alkur'ani mai girma da sojojin Amurka su ka yi, a yayin zanga-zangar da aka yi a jiya a gundumar Qunduz mutane hudu ne su ka kwanta dama yayin da wasu hamsin su ka jikkata.
Har ila yau wani mutum guda ya kwanta dama a garin Lagman da ke gabacin kasar ya yi da wasu ashirin su ka sami raunuka, wasu mutane uku a gundumar Logar sun rasa rayukansu sai kuma wasu mutane biyu da su ka jikkata.
A gundumar Wardak ma an kashe mutum guda da kuma jikkata wasu da dama, a jiya asabar ne dai mutanen Afghanistan su ka cika kwanaki biyar a jere suna yin zanga-zanga domin yin tir da keta hurumin alkur'ani mai girma da sojojin Amurka su ka yi ta hanyar kona shi. 960420