Bangaren kasa da kasa, jamiyyar Hizb Islami a kasar Iraki ta yi kakkausar suka kan keta alfarmar kur'ani mai tsarki da sojojin mamayar Amurka suka yi a kasar Afghanistan da nufin tozarta musulmi da addinin muslunci.
Rahotannin da suke fitowa daga kasar Afghanistan suna nuni da cewa wasu masu zanga-zanga uku sun yi shahada a yau sakamakon bude musu wuta da jami’an tsaron kasar suka yi a ci gaba da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da kona Alkur’ani mai girma da sojojin Amurka suka yi a sansaninsu na Bagram a ranar talatar da ta gabata.
Rahotannin sun ce dubun dubatan masu zanga-zangar suna ci gaba da fitowa a garuruwa daban-daban na kasar Afghanistan don nuna rashin amincewarsu da wannan danyen aikin da sojojin Amurkan suka yi.
Aalal akalla mutane uku sun rasa rayukansu a yau sannan wasu biyu kuma sun sami raunuka a lardin Logar sakamakon bude musu wuta da jami’an tsaro suka yi.
Baya ga kasar Afghanistan din a kasashe daban-daban na duniya ma irin su Pakistan, Yemen, Bahrain da sauransu al’ummomi suna ci gaba da fitowa kan tituna don nuna rashin amincewarsu da wannan danyen aikin.
960414