IQNA

Kungiyar Hizbullah Za Ta Gudanar Da Taro Mai Taken Qods Babban Birnin Palastine

20:27 - March 03, 2012
Lambar Labari: 2284713
Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmayar muslunci ta hizbullah a kasar Lebanon za ta shirya gudanar da wani zaman taro mai taken birnin Qods babban birnin larabawa da musulmi da palastinawa baki daya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa, a cikin makonan kungiyar gwagwarmayar muslunci ta hizbullah a kasar Lebanon za ta shirya gudanar da wani zaman taro mai taken birnin Qods babban birnin larabawa da musulmi da palastinawa baki daya wanda za a gudanar a birnin Beirut na kasar Lebanon.
Za a gudanar da wannan taro ne abbabn dakin taruka na risalat da ke birnin Beirut, tare da halartar daruruwan masana da marubta gami da malamai da ‘yan jarida, inda za a gabtar da jawabai da suka danganci masallacin Qods da kuma birnin baki daya, da matsayinsa ga musulmi da larabawa, da kuma mabiya addinin kirista, wadanda su ma suna da wurare da suke girmamawa acikin wannan birni mai albarka.
Wannan mataki dai ya zo ne a daidai lokaci da yahudawan sahuniya suke ta kokarin rushe masallacin mai alfarma, tare da mayar da birnin baki dayansa mallakin yahudawan sahyuniya.
Kwamitin shirya zaman taron wanda ke mara baya ga gwagwarmayar palastinawa, ya bayyana cewa duk masu bukatar halartar taron kofa abude take a gare su.
963677
captcha