IQNA

Makaman Gwagwarmaya Hakki Ne Na Lebanon Domin Fuskantar Barazanar Isra’ila

20:27 - March 03, 2012
Lambar Labari: 2284716
Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmayar muslunci a kasar Lebanon ta hizbulla ta fitar da wani bayani da acikinsa take mayar da martani kan furucin sakataren majalisar dinkin duniya dangane da makaman kungiyar, inda bayanin ya ce hakkin lebanon ta mallaki makamai na gwagwarmaya domin mayar da martani kan duk wani shishin Isra’ila.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya naklato daga shafin sadarwa na ayanr gizo na tashar talabijin din Alamanr cewa, gwagwarmayar muslunci a kasar Lebanon ta hizbulla ta fitar da wani bayani da acikinsa take mayar da martani kan furucin sakataren majalisar dinkin duniya dangane da makaman kungiyar, inda bayanin ya ce hakkin lebanon ta mallaki makamai na gwagwarmaya domin mayar da martani kan wuce gonda irin yahudawan sahyuniya kan al’ummar Lebanon.
A cikin bayanin kungiyar ta yi kakkausar suka kan abin da ta kira rashin lamiri na mutumin da ake kira sakataren majalisar dinikin duniya, wanda ya kamata ya kare hakkokin mutane na kasashen duniya, amma maimakon hakan sai mayar da hankali wajen kare barnar da yahudawan sahyuniya suke aikatawa, tare da ba su kariya ta hanyar yin amfani da kujerarsa.
A lokutan baya ne Ban ki moon ya bayyan acewa, makaman da kungiyar gwagwarmayar muslunci ta hzibullah take mallaka barazana ce ga ita kanta kasar Lebanon.
963659
captcha