Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, jagoran juyin juya halin muslunci yana da babban tasiri a cikin motsin al'ummomin yankin gabas ta tsakiya wadanda suke neman 'yanci da kuma hakkokinsu da azzalauman sarakuna suka haramta musu a matsayinsu na 'yan kasa.
Dangane da zaben da aka gudanara kasar kuwa, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada wajibcin da ke cikin fitowar al'ummar kasar a zaben 'yan majalisa da za a gudanar nan gaba yana mai cewa zaben na wannan karon yana da matukar muhimmanci. A gobe juma'a ne ake sa ran al'ummar Iran za su fito don kada kuri'unsu a zaben 'yan majalisa kasar karo na tara da za a gudanar.
Tun bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran kimanin shekaru talatin da uku da suka gabata, ana iya cewa a kan gudanar da zabe alal akalla sau guda a kowace shekara, kama daga na shugaban kasa ko na 'yan majalisar shawarar Musulunci ko na kwararru da dai sauransu sannan kuma irin fitowar da mutane suke yi don kada kuri'unsu lamari mai ban mamaki musamman ga kasashen yammaci wadanda suke iyakacin kokarinsu wajen ganin sun kashe wa al'ummar Iran din gwuiwa da hana su fitowa.
Tsawon wadannan shekarun dai Amurka da kawayenta sun yi dukkanin abin da za su iya ta hanyar kafafen watsa labarai da sauran hanyoyin farfagandarsu wajen ganin al'ummar Iran ba su fito kwansu da kwarkwatarsu don kada kuri'un na su ba. Manufar hakan kuwa ita ce don su nuna wa duniya cewa al'ummar Iran sun fara kosawa da tsarin Musulunci na kasar.
A saboda haka ne ake ganin fitowar al'ummar Iran da dukkan karfinsu a yayin duk wani zaben da aka gudanar a kasar, baya ga batun ayyana makomarsu da kuma zaban wadanda za su aiwatar musu da abin da suke so, har ila yau kuma akwai wani sako mai muhimmanci cikin hakan ga ma'abota girman kan duniya. Wannan sakon kuwa shi ne tabbatar da azamar da suke da ita wajen ci gaba da riko da tsarin Jamhuriyar Musulunci da ke iko a kasar.
960491