Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: an gudanar da wani gagaramin taron girmama yan mata mahardata kur'ani mai girma karkashin cibiyar OOVTaDah a garin Nuchehar na kasar Turkiya kuma an gudanar da wannan buki ne a babban dakin taro na kabadukiya a garin. Wannan taro nafara shi ne tare da karatun kur'ani mia girma daga makaranci kuma mahardacin kur'ani Sheikh Jamil Asta yayin da a ci gaban wanna taron babban malamin kuma mai bayar da fatawa a garin Yakub Aztark ya gabatar da jawabi kan muhimmanci da falalar da ke tattare da karatun kur'ani da kuma harder karatun kur'ani mai girma. Daga bisani an gabatar da ainafin abin day a tara mutane a wannan guri wato an fara kiran mahardata kur'ani yan mata domin girmama masu kan himmar da suka nuna ta harder kur'ani mai girma da kuma yadda suka kasance daga cikin wadanda suka samu dacewa da harder kur'ani mai girma da fatar ganin sun ci gaba da yin riko da wannan hanyar tare da yi masu fatar dacewa a rayuwar ta yau da kullum. Daga cikin yan makaranta dari da saba'in ne aka samu yan mata masu harda a wannan makaranta ashirin da suka kammala da kuma aka girmama su a wannan taron.
964501