Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CPI cewa, wasu daga cikin fitattun mamaln addini da kuma masana a sassa na duniya suna ci gaba da yin kira ga dukaknin mabiya addinai musamman na kiristanci da musulunci das u gudanar da gagarumar zanga-zanga a ko'ina cikin fadin duniya nuna goyon baya ga masallacin Qods mai alfarma, wanda ahalin yanzu yake fuskantar barazanar rushewa daga yahudawan sahyuniya.
Palastinawa 13 ne suka yi shahada a wasu hare-haren ta'addanci da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a yankuna daban-daban na yankin Zirin Gaza, tare da jikkatar wasu da dama.
Mai aiko ma gidan talabijin din presstv rahotanni daga Zirin gaza ya habarta cewa, hare-haren na sojin yahudawan sahyuniya kan al'ummar yankin Gaza sun tsananta ne a daren jiya, bayan kai wasu hare-haren da rana da suka yi sanadiyar yin shahadar mutane hudu, yayin da a daren jiya wasu Karin 9 suka yi shahada a daren jiya, wasu da dama da suka hada da mata da kanan yara kuma sun samu raunuka.
Haramtacciyar kasar Isra'ila ta fara tsananta hare-harenta kan al'ummar palastinu da nufin fadada mamayarta a cikin yankunan palastinawa, ba tare da kasashen yammacin turai da na larabawa sun ce uffan kan wannan ta'asa ba.
968314