Bangaren kasa da kasa, bababn malamin addinin muslunci na jami'ar azhar da ke birnin Alkahira na kasar masar Sheikh Ahamd Tayyib ya bayyana cewa, makiya musulunci sun samu wurin zama ne bayan da musumi suka rarraba, amma da musulmi za su hadi da makiya sun tarwatse.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Akhbarul yaum cewa, babban malamin jami'ar Azhar ta kasar Masar Sheikh Ahmad Tayyib ya bayyana cewa, Haramtacciyar kasar Isra'ila tana ci gaba da wanzuwa sakamakon rarrabar da ke akwai tsakanin musulmi, kuma hakan shiri ne na makiya musulunci domin su ci gaba da zama masu juya musulmi da larabwa da kuma arzikinsu.
Sheikh Ahmad Tayyib ya sheda hakan ne a lokacin da yake ganawa da wata tawagar masana Iraniyawa da suke gudanar da ziyara akasar Masar, inda ya bayyana cewa yahudawan sahyuniya su ne suke azuzuta rikicin mazhaba tsakanin musulmi, abun ban takaici kuma wasu musulmin sun fada a cikin wannan tarko su ne suke yi wa yahudawan wannan aiki.
Shehin malamin ya kara da cewa, da musulmi za su gane makircin da yahudawan sahyuniya da 'yan korensu suke kitsawa musulunci da musulmi a duniya, da sun dunke duk wata Baraka a tsakaninsu, domin kuwa babban makiyin musulmi daya ne, shi ne tunani da akidar sahyuniyanci da ke juya manyan kasashen duniya, kuma babbar cibiyar wannan akida ita ce.
Da dama daga cikin masana sun yi imanin cewa wasu daga cikin shugabannin kasashen musulmi sun zama 'yan koren yahudawan sahyuniya, inda suke aiwatar da dukaknin abin da makiya suka kullawa musulmi domin rarraba kansu , ta yadda yahudawa za su karensu babu babbaka.
968280