IQNA

Ana Ci Gaba Da Yin Allawadai Da Hare-Haren Ta'addancin Isra'ila Kan Al'ummar Gaza

19:58 - March 12, 2012
Lambar Labari: 2290612
Bangaren kasa da kasa, al'ummomin duniya gami da gwamnatoci masu 'yancin siyasa suna ci gaba da yin Allawadai da hare-haren ta'addancin da haramtacciyar kasar Isra'ila take cig a da kaiwa kan al'ummar yankin zirin gaza a cikin lokutannan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dilllancin labaran wam na kasar hadaddiyar daular larabawa cewa, , al'ummomin duniya gami da gwamnatoci masu 'yancin siyasa suna ci gaba da yin Allawadai da hare-haren ta'addancin da haramtacciyar kasar Isra'ila take cigaba da kaiwa kan al'ummar yankin zirin Gaza.
Ana ci gaba da Allah wadai da sabbin hare-haren da HKI ta kaddamar a kan al'ummar Gaza cikin 'yan kwanakin nan da ya yi sanadiyyar shahadar wani adadi mai yawa na Palastinawan.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran cikin wata sanarwa da fitar a yau din nan ta yi Allah wadai da wadannan hare-haren ta'addancin da HKI ta kaddamar kan Gazan kamar yadda kuma ta yi Allah wadai da irin halin ko in kula din da cibiyoyin kasa da kasa suke nunawa lamarin. A kasar Turkiya ma al'umma da 'yan kungiyoyi kare hakkokin bil'adama sun gudanar da zanga-zangar kin jinin HKI a birnin Ankara don nuna rashin jin dadinsu da wadannan hare-hare na ta'addanci da kuma kiran cibiyoyin kasa da kasa su yi wani abu wajen dakatar da wannan danyen aikin.
A Zirin Gazan ma dubun dubatan al'ummomin birnin sun fito don Allah wadai da wannan danyen aiki na yahudawan sahyoniyan inda suka bayyana shirinsu na mayar da martani ga wannan danyen aikin.
Tun daga shekaran jiya juma'a ne dai HKI ta fara kai irin wadannan munanan hare-hare lamarin da ya zuwa yanzu ya yi sanadiyyar shahadar kimanin mutane 18 da kuma raunana wasu da dama.
969340
captcha