IQNA

Kungiyoyi Da Ma'aikatu A palastinu Suna Nuna Goyon bayansu Ga Al'ummar gaza

19:58 - March 12, 2012
Lambar Labari: 2290614
Bangaren kasa da kasa, yau kimanin kwanaki uku kenan a jere sojojin yahudawan sahyuniya suke ci gaba da kaddamar da hare-haren ta'addanci kan al'ummar yankin zirin Gaza bha tare da kasashe da gwamnatoci sun bayyana damuwarsu kan hakan ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na kamfanin dilalncin labaran palastinu an Ma'a cewa, kimanin kwanaki uku kenan a jere sojojin yahudawan sahyuniya suke ci gaba da kaddamar da hare-haren ta'addanci kan al'ummar yankin zirin Gaza bha tare da kasashe da gwamnatoci sun bayyana damuwarsu kan hakan ba saboda mutuwar zuciya da rashin lamiri.
Bayanin ya ci gaba da cewa babbar hadakar ma'aikata a yankin khalil da ke cikin gabar yammada kogin Jordan a palastinu ta sanar cewa, tan agoyon bayan al'ummar palastinu marassa kariya da suke ci gaba da fuskantar shiahigi da yahudawan sahyuniya a cikin wadannan lokuta, inda mutane sam da ashirin suka rasa rayukansu.
Yanzu haka da an share kimanin kwanaki uku a jere sojojin yahudawan sahyuniya suna ci gaba da kaddamar da hare-haren ta'addanci kan al'ummar yankin zirin Gaza, tare da kasha mata da kanan yara da suke zaune a yankin.
Da dama daga cikin masu bin diddigin lamuran da suke kai da komowa sun yi amannar cewa, haramtacciyar kasar Isra'ila tana huce haushinta ne na rashin samun goyon baya na kai hari kan Iran a ka palastinawa.
969395
captcha