IQNA

Kungiyar Hadin Kan Musulmi Ta yi Allah wadai Da Harin Da HKI Ta Kai Wa Gaza

18:42 - March 13, 2012
Lambar Labari: 2291281
Bangaren kasa da kasa: kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar ashirin da daya ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ta fitar da bayanin yin allah wadai da sojojin Haramtacciyar kasar Isra'ila da sojojinta suka kai wa fararen hula dab a su dauke da makamai harin a yankin Zirin Gaza.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: : kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar ashirin da daya ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ta fitar da bayanin yin allah wadai da sojojin Haramtacciyar kasar Isra'ila da sojojinta suka kai wa fararen hula dab a su dauke da makamai harin a yankin Zirin Gaza.An nakalto daga majiyar kungiyar hadin kan kasashen musulmi OCI KO OIC cewa; Ikmalul Dine Ihsan Uglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi a cikin wani bayani da sanarwa day a fitar ya yi kaukausar suka da dirar mikiya kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila masu wuce gonad a iri da aiwatar da ta'addanci da zalunci kan faraen hula a yankin zirin gaza.Sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila dai sun kai harin zalunci kan fararen hula ayankin zirin gaza day a yi sanadiyar shahadar fararen hula sha biyu da kuma jikkata wasu da daman gaske da cewa wannan wani take hakkin dan adam ne a fili karara ko shakka babu.
970209
captcha