Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na wam na kasar hadaddiyar daular larabawa cewa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya da kuma kungiyar hadin kan kasashen larabawa sun gudanar da wani zama na hadin gwiwa domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya da kum arikice-rikicen da suke faruwa a ynakin da hanyoyin shawo kansu.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan zaman tattaunawa ya tabo batutuwa da dama da suka hada da hankoron da wasu daga cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya suke na ganin cewa sun kara karfafa dangantakarsu da haramtacciyar kasar Isra’ila, a daidai lokacin da take ci gaba da yin kisan gilla kan al’ummar palastinu ba tare da tsagaitawa ba.
Kasashen Saudiyya da Qatar gami da Jordan a halin yanzui su en suka fi dukaknin kasashe kusanci da haramtacciyar kasar Isra’ikla atsakanin kasashen larabawa, kuma su ne aka baiwa kwangilar tarwatsa Syria, ta yadda gwamantin yahudawan sahyuniya za ta ci gaba da fadada karfinta da samuwarta a yankin gabas ta tsakiya, wanda kuma Syria ce ke kawo ma ta cikas kan hakan.
Wadanan kungiyoyi na hadin kan kasashen musulmi ta duniya da kuma kungiyar hadin kan kasashen larabawa sun gudanar da wannan zama na hadin gwiwa ne domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, amma kuma ba su cimma komai ba har suka watse.
970643