IQNA

Ofishin Jakadancin Amurka A Lebanon Ya Zama Wurin Leken Asirinta Kan Syria

21:01 - March 13, 2012
Lambar Labari: 2291317
Bangaren kasa da kasa, mataimakin shugaban kwamitin shawara na kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ya bayyana cewa ofishin jakadancin Amurka dake birnin Beirut fadar mulkin kasar ya zama wani leken asiri kan kasar Syria da kuma shirya mata makarkashiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almanar cewa, Sheikh Nabil Kawuk mataimakin shugaban kwamitin shawara na kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ya bayyana cewa ofishin jakadancin Amurka dake birnin Beirut fadar mulkin kasar ya zama wani leken asiri kan kasar Syria da kuma shirya mata makarkashiya domin kara a zuzuta wutar rikici a cikin kasar, wadda dama Amurka da karnukan farautarta ne suka kirkiro shi.

Bayanin ya ci gaba da cewa muatne da dama a kasar ta Leabanon suna nuna matykar damuwa kan halin da ake ciki a halin yanzu akasar Syria, kasantuwar kasashen biyu suna da dangataka da juna ta tsawon shekaru da babu wanda zai iya raba su, duk kuwa da hankoron da kasashen turai suke yi na ganin cewa sun rab adukkanin kasashen larabawa da kasar Syria, domin kwa ita kadai ce ba ta shiri da su kuma ta hana su kaiwa ga burinsu na rarraba kasashen larabawa.

Sheikh Nabil Qawuk mataimakin shugaban kwamitin shawara na kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ya bayyana cewa ofishin jakadancin Amurka dake birnin Beirut fadar mulkin kasar ya zama wani leken asiri kan kasar Syria da kuma shirya mata makirci.

970280










captcha