Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, daya daga cikin masana acikin kasashen larabawa ya bayyana cewa kisan kiyashin da sojojin mamayar Amurka suke yi kan fararen hula akasar Afghansitan ya kara jawo musu bakin jini na shan kakkausar suka daga al’ummar kasar da kuma sauran al’ummomin duniya masu lamairi, kuma ficewrsu ce kawai hanyar kawo karshen wannan rikici da suka jawo kan al’ummar wannan kasa ta musulmi.
Ya ce kasa da makonni 3 da keta alfarmar kur'ani mai tsarki ta hanyar kone shi da sojojin mamayar Amurka suka yi a kasar Afghanistan, sojin na Amurka sun sake tafka wata ta'asar da ta kara fito da dabi'arsu ga al'ummar kasar Afghanistan da sauran al'ummomin duniya baki daya, inda daya daga cikinsu ya yi kisan gilla a kan fararen hula 18 a lokacin da suke barci a cikin gundimar Kandahar a Lahadin da ta gabata.
Mutanen kauyen Panjwai da ke cikin gundumar Kandar da ke kudancin kasar Afghanistan sun sheda cewa, sojan na Amurka ya biyo dare ne, a lokacin da ya balle kofofin gidaje uku a kauyen a lokacin da mutane suke barci, inda ya bude wuta kansu, a nan take ya kashe fararen hula 17 da suka hada da mata da kananan yara, ya kuma jikkata wasu da dama.
Wannan mummunan aikin ta'addanci ya jawo fushin al'ummomin kasar ta afganistan da ma sauran kasashen duniya, inda har yanzu ake ci gaba da yin Allawadai da gwamnatin Amurka da kuma ayyukanta na ta'addanci kan fararen hula a kasar Afghanistan.
A wani mataki na borin kunya, bayan da dukkanin al'umomin duniya suka samu bayanin abin da ya faru, rundunar tsaro ta NATO ta yi kokarin nisanta kanta da wannan danyen aiki, tare da dora alhakin hakan kan sojan na Amurka, yayin da shi kuma shugaban kasar ta Amurka Barack Obama ya sheda wa shugaban kasar Afghanistan cewa za gudanar da bincike kan lamarin, duk kuwa da cewa har yanzu ba a san dalilin da ya sanya sojan na Amurka yin wannan kisan gilla kan wadannan fararen hula ba, amma shugaban kasar ta Afghanistan ya yi Allawadai da hakan, tare da bayyana cewa wannan mummunan aiki ba abu ne da al'ummar Afghanistan za su yafe shi ba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da sojojin Amurka suke aikata irin wannan aiki na ta'addanci kan fararen hula a kasar Afghanistan ba, domin kuwa sun yi hakan ya fi kudin taro a kasar ta Afghanistan da ma kasar Iraki, inda sukan kashe fararen hula marassa kariya, kuma su wulakanta gawawwkinsu, ta hanyar konewa ko yin bawali a kansu da dai sauran ayyuka na tozarci wadanda suka yi hannun riga da dukaknin dokoki na kasa da kasa da ma 'yan adamtaka.
A wannan karon dai ga dukaknin alamu Amurka ta debo ruwan da za a dafa ta da shi ne, domin kuwa wannan aikin ta'addanci ya zo 'yan makonni bayan keta alfarmar kur'ani mai tsarki, lamarin da ya bakanta wa dukkanin musulmin duniya rai, kuma ta ga matsanancin fushin al'ummar Afghanistan kan hakan.
972134