IQNA

Al'ummar Baharain Na Ci Gaba Da Zanga-Zangar Lumana Domin Neman hakkokinsu

16:03 - March 17, 2012
Lambar Labari: 2293082
Bangaren kasa da kasa, al'ummar kasar Bahrain sun bukaci dakarun mamaya na kasar Saudiyya da su fice daga kasar, bayan da suka kwashe shekara guda suna taimakama masarautar kasar wajen murkushe fararen hula masu zanga-zangar lumana.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bahrain revolution news cewa al'ummar kasar Bahrain sun bukaci dakarun mamaya da su fice daga kasar, bayan da suka kwashe shekara guda suna taimakama masarautar Ali-khalifa wajen murkushe fararen hula masu zanga-zangar lumana kuma marassa kariya a fadin kasar.
A wani jawabi da ya gabatar a gaban dubban daruruwan mutane da suka taru a kusa da birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain, Sheikh Ali Salman shugaban jam'iyar Al-wifaq jam'iyyar adawar siyasa mafi girma a kasar, ya bayyana cewa da ya kamata ne Saudiyya ta zama mai shiga tsakani domin warware matsalar al'ummar Bahrain, maimakon ta zama daya daga cikin bangarorin rikicin.
Sheikh Salman ya ce yin amfani da karfi da masarautar Bahrain ke yi kan fararen hula masu zanga-zangar lumana, tare da taimakon sojojin Saudiyya, babu abin da zai kara sai fusata jama'a da kuma kara musu kaimi wajen ci gaba da borensu, domin kuwa abin da mutanen kasar suke bukata shi ne, sarki ya ci gaba da sarautarsa, amma mutane ke da hakkin zaben 'yan majalisa da za su zabi fira ministan, maimakon sarki ya zabi 'yan majalisa da kansa kuma ya nada fira ministan da ya ga dama, ba tare da nuna banbanci tsakanin al'ummar kasar ba.
972903
captcha