Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakato daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, masu zanga-zanga a kasar masar sun yi wa ofishin jakadancin kasar Amurka da ke birnin Alkahira kawanya domin nuna rashin gamsuwarsu da abin da kasar take yin a shigar shugula cikin harkokin masar tare da yin kira da akori jakadan kasar ta Masar baki daya.
A wani labarin kuma Shugaban darikar Orthodoxe na kasar Masar, Chenuda na 3 ya rasu jiya asabar yana da shekaru 88, wannan jagoran addinin mai mabiya sama da million 12 a kasar ta Masar, shi ke rike da matsayin paparoma na 117 na Alexandrie tun 1971.
Mutuwar wannan jagoran addinin kirista ta girgiza jama'ar kasar ta Masar nasu yawa mabiya darikar Orthodxe da ma wasu musulmin. Chenouda yayi gwagwarmaya mai dama da tsofon shugaban kasar ta Masar Anouar Sadate game da yarjejeniyar sulhun da ya sa ma hannu tsakaninsa da HKI a 1979, hulda tsakanin mabiya dakirar ta copte ta daidaita a lokacin Hosni Mubarack.
Don haka ake ganin cewar wanda zai gaje shi na da mahimmiyar rawar da zai taka a tafiyar siyasar kasar ta Masar a wannan lokaci na rikon kwarya. Babban Imamin jamia'ar Azhar Cheik Ahmed El Tayib, ya maika gaisuwar ta'aziyarsa, yana cewa kasar Masar ta yi rishi, saboda ya dauki batun birnin qudus da gwagwarmar Palesdinawa da mahimmanci saosai. Haka shima shugaban jam;iyar yan uwa musulmi mafi rinjaye a Masar Mohamed Moursi, ya isar da gaisuwar ta'aziyarsa, yana yaba kokarin da mariganyin yayi ga kasar Masar. 973119