IQNA

Ana Shirin Gudanar Da Zanga-Zanagar Nuna Goyon Baya Ga Al’ummar Palastinu A London

20:06 - March 25, 2012
Lambar Labari: 2294599
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da wata gagarumar zanga-zangar nuna cikakken goyon bay aga al’ummar palastinu a gaban ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na palestine info cewa, yanzu haka ana shirin gudanar da wata gagarumar zanga-zangar nuna cikakken goyon bay aga al’ummar palastinu a gaban ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya domin tabbatar wa duniya cewa masu lamiri a cikin mutane ako’in acikin duniya ba su goyon bayan abin da ake yi a kana fararen hula palastinawa.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gangamin dai babbar cibiyar palastinawan Birtaniya ce ta shirya shi, kuma zai samu halartar wakilan cibiyoyin fararen hula da kuma kungiyoyi na addini, gami da lauyoyi da kuma masu kare hakkokin bil adama da suke da cibiyoyi a birnin London da ma wasu sassa na kasar.
Shirin gudanar da gagarumar zanga-zangar nuna cikakken goyon baya ga al’ummar palastinu a gaban ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya wata babbar manuniya ce ta yunkurin al’ummomin duniya da kuma farkawarsu kan babakeren yahudawan sahyuniya.
974740


captcha