IQNA

Kasashen Yammacin Turai Na Shrin Kawo Yakin Basasa A Kasar Syria

22:21 - March 29, 2012
Lambar Labari: 2295722
Bangaren kasa da kasa, kasashen yammacin turai na hankoron ganin sun kawo yakin basasa a cikin kasar Syria ta hakan zai baiwa haramtacciyar kasar Isra’ila ci gaba da cin karenta babu babbaka a yankin wadda kuma take fuskantar barazana daga kasasar ta Syria a kowane lokaci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, da dama daga cikin masana sun ammanar cewa kasashen yammacin turai na hankoron ganin sun kawo yakin basasa a cikin kasar Syria, ta yadda hakan zai baiwa haramtacciyar kasar Isra’ila ci gaba da cin karenta babu babbaka a yankin wadda kuma take fuskantar barazana daga kasasar ta Syria a kowane lokaci saboda matsayinta na kishin al’ummar larabawa.
Kasar Syria ita kadai ce daga cikin kasashen larabawa da haramtacciyar kasar Isra’ila take kallonta a mtasyin barazana, saboda haka faduwar Bashar Asad babbar riba ce gare tasaboda yin hakan zai ba ta damar ci gaba da aiwatar da abin da tashirya na samar wanoi sabon yanayi a yankin gabas ta tsakiya baki daya, ta yadda za ta zama babbar daula mai cikakaen iko kan sauran dukaknin kasashen yankin.
Masana da dama sun yi imanin cewa kasashen yammacin turai na hankoron ganin sun kawo yakin basasa a cikin kasar Syria ta hakan zai baiwa haramtacciyar kasar Isra’ila ci gaba da cin karenta babu babbaka a yankin wadda kuma take fuskantar barazana daga kasasar ta Syria a kowane lokaci kamar dai yadda alamu suke nuni.
975638

captcha