IQNA

Ganawar Malaman Addinan Muslunci Da Kiristanci A Yankin Jubail Na Lebanon

21:44 - March 31, 2012
Lambar Labari: 2296072
Bangaren kasa da kasa, jagororin mabiyan addinan kiristanci da muslunci a yankin Jubail na kasar Lebaon sun gana a babban ginin majami’ar Sin Jan da ke yankin dangane muhimman batutuwa da suka danganci bangarorin biyu da za su taimaka wajen kara samun fahimtar juna.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lorientlejour cewa, jagororin mabiyan addinan kiristanci da muslunci a yankin Jubail na kasar Lebaon sun gana a babban ginin majami’ar Sin Jan da ke yankin dangane muhimman batutuwa da suka danganci bangarorin biyu da za su taimaka wajen kara samun fahimtar juna a tsakaninsu.
Taron tsakanin bangarorin biyu ya gamsar da masu halatarsa, bisa la’akari da irin yadda kasar Lebanon ta zama wurin buga misali na fahimtar juna tsakanin mabiya addinan kirsitanci da muslunci, duk kuwa da yakin basasa da bangarorin biyu suka yi a lokutan baya wanda aka jaza musu da nufin wargaza su, amma kuma hakan sai ya zama wani dalili na hada kansu.
Manyan jagororin mabiyan addinan kiristanci da muslunci a yankin Jubail na kasar Lebaon sun gana a babban ginin majami’ar Sin Jan da ke yankin dangane muhimman batutuwa da suka danganci bangarorin biyu da za su taimaka wajen kara samun fahimtar juna mai dorewa.
976444


captcha