Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmaya ta jabha a yankin palastinu ta tabbatar da cewa yin gwagwarmaya da yin tsayin daka shi ne kawai hanyar dawo da hakkokin palastinawa da kuma bayar da kariya gare su da kuma dawo da wurare masu tsarki yahudawan sahyuniya suka kwace musu.
Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin diln Almanar cewa, kungiyar gwagwarmaya ta jabha a yankin palastinu ta tabbatar da cewa yin gwagwarmaya da yin tsayin daka shi ne kawai hanyar dawo da hakkokin palastinawa da kuma bayar da kariya gare su da kuma dawo da wurare masu tsarki yahudawan sahyuniya suka kwace musu tun tsawon shekaru da suka gabata.
A bangare guda kuma a ci gaba da mayar da martanin da malaman addinin muslunci gami da masana suke yi kan malamin gwamnatin Qatar Yusuf Kardawi, ministan mai kula da harkokin addinin muslunci a palastinu Muhmud Habbash ya bayyana cewa fatawar da Yusuf Kardawi ya bayar da ke hana sauran musulmi ziyartar masallacin Qods mai alfarma ta sabawa koyarwar alkur’ani mai tsarki da kuma sunanr manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
Kwanakin baya ne Yusuf Kardawi da ake kallonsa amtsayin daya daga cikin mamalan duniyar sunna, kuma daya daga cikin malaman da suka taka rawa a baya domin ganin sun wayar da kan muslulmi kan babbar barazanar da ke tattare da kulla alaka da musulmi suke yi da haramtacciyar kasar Isra’ila, amma a halin yanzu ya zama malamin fadar sarkin Qatar, inda yake bayar da fatawowyi da suka yi daidai da abin da sarkin kasar ke bukatar ji, kasantuwarsa daya daga cikin karnukan farautar yahudawa.
976393