Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shfain sadarwa na yanar gizo cewa, masarautar kasar Bahrain karakshin mulkin gidan khalifa suna yin abin da haramtatcciyar kasar Isra’ila ma ba ta yi na tsabar zalunci da danne hakkkokin mutanen kasar marassa kariya kamar yadda kuma sauran kasashen dunbiya suke ba ta kariya kan wannan ta’addanci kan fararen hula.
Mahukunta a kasar Bahrain sun sako 'yar mai rajin kare hakkokin bil'adama na kasar Abdulhadi al-Khawaja, wato Zainab al-Khawaja daga gidan yari bayan da kama ta da kuma ci gaba da tsare ta na kwanaki da jami'an tsaro suka yi.
Lauyan Zainab al-Khawajan ne ya sanar da hakan inda ya ce jami'an tsaron sun sako ta bayan kwanaki suna tsare da ita sakamakon shiga cikin zanga-zangar da al'ummar kasar suka shirya don a saki mahaifinta wanda mahukunta suka yanke masa hukumcin daurin rai da rai sakamakon shirya zanga-zangar neman sauyi a kasar da mahukunta suka ce wani kokari ne na kifar da gwamnatin kasar.
Yayin da ya ke magana kan yanayin da Abdulhadi al-Khawajan, wanda yake ci gaba da yajin cin abin na tsawon watanni biyu, Lauyan yace yana cikin mawuyacin hali ainun. 'Yan adawa a kasar Bahrain din dai sun ja kunnen mahukuntan da su guji abin da zai biyo baya matukar dai al-Khawajan ya rasu sakamakon yajin cin abincin da yake yi.
979363