Bangaren siyasa ;ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Ahmad Wahidi ya ja kunnen kasashen Tekun Fasha dangane da amincewa da shawarar da Amurka ta gabatar musu na kafa garkuwa kakkabo makamai masu linzami na hadin gwuiwa a tsakaninsu yana mai cewa hakan wani kokari ne da Amurka take yi wajen ba da kariya ga HKI da kuma samun ci gaba da tabbatar da mulkin mallakar Amurka da HKI a wannan yankin.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kuma da harkokin kur'ani mai girmna a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Janar Wahidin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai da ya yi kan wannan batu inda ya kirayi kasashen yankin Tekun Fasha da kada su yarda su sanya kansu cikin wannan tarko na Amurkan.
A kwanakin baya ne dai sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, a wani taro da ta yi da ministocin harkokin wajen kasashen Tekun Fashan, ta gabatar musu da wannan shawara ta kafa wannan garkuwa ta kakkabo makamai masu linzami don fada da abin da ta kira 'ci gaba da barazanar da Iran take musu'.
Da dama daga cikin masana dai suna ganin manufar wannan shawarar ita ce kare HKI da kuma ba ta damar ci gaba da zalunci da babakeren da take yi wa kasashen gabas ta tsakiya da kudaden kasashen larabawan.
981784