Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na swissinfo cewa, Kherat Shatir dan takarar neman shugabancin kasa na kungiyar Ikhwan akasar Masar ya bayyana cewa tsayawar takara da mataimakin tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Masar Umar Sulamin ya yi wani babban cin zarafi ne ga juyin al'ummar kasar wanda hakan ne ya ba su damar kafa tsari na demokradiyya.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar Masar na hambararriyar gwamnatin Husni Mubarak wato Umar Suleiman ya sanar da tsayawa takara a zaben shugaban kasa da za a gudanar a kasar a watan Mayu. Wannan sanarwa ta Umar Suleiman na aniyar kai wa ga shugabancin kasar Masar tamkar yunkurin karshe ne daga bangaren masu kokarin karya juyin juya halin da al'ummar kasar suka yi, wanda ya yi nasarar kawar da gwamnatin Husni Mubarak.
A shekarar 1991 gwamnatin Husni Mubarak ta nada Umar Suleiman mataimakin darektan hukumar leken asirin sojan kasar, a shekarar 1993 kuma ya zama shugaban babbar hukumar leken asirin kasar. A ranar 29 ga watan Janairun 2011 a lokacin da boren juyin juya hali ya yi kamari a kasar Masar Husni Mubarak ya nada shi mataimakin shugaban kasa.
Umar Suleiman na hannun daman Husni Mubarak ne kut-da-kut har ma wasu kungiyoyin kare hakkin bil Adama suke kiransa da sunan "Mubarak na Biyu" saboda kasancewarsa yana da hannu a zalunci da kama karya da Husni Mubarak ya aikata.
Saboda sanin tarihinsa da rawar da ya taka a cin zarafin alumma da take hakkoin dan Adam hatta a lokacin yunkurin juyin juya hali, jamaar kasar Masar sun yi zanga zanga don nuna fushinsu da sanarwar da Umar Suleiman ya yi na cewa zai tsaya takarar zaben shugaban kasa.
981393