Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almanar cewa, kungiyar gwagwarmayar muslunci ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakkausar suka tare da yin Allawadai da kashe dan jaridar kasar Lebanon da ‘yan tawayen kasar Syria suka yi a lokacin da yake daukar hotunan ‘yan ta’adda suna shiga cikin kasar Syria dauke da makamai daga Lebanon wadanda yaran Amurka da suke cikin kasar Lebanon suke ba su.
A bangare guda kuma a yau ne ministan harkokin wajen kasar Syria zai gana da jami'an gwamnatin kasar Rasha, domin tattuna muhimman batutuwa da suka danganci alaka tsakanin kasashen biyu da kuma rikicin da ake yi a kasar, kamfanin dilalncin labaran sana na kasar Syria ya bayar da rahoton cewa, daga cikin wadanda ministan harkokin wajen Syria Walid Mu'allim zai gana da su yau a birnin Moscow har da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergie Lavrov, inda za su yi dubi kan yanayin da ake ciki a kasar, da kuma batun shawarwarin da tsohon sakatare janar na majalisar dinikin duniya Kofi Annan ya gabatar domin warware rikicin na Syria.
A bangare guda kuma rahtanni sun tabbatar da cewa rundunar sojin Syria ta kwace babban asibitin birnin Homs daga hannun 'yan bindiga da suke mamaye da shi tsawon kwanaki, inda suka yi garkuwa da jami'an kiwon lafiya da marassa lafiya, sojojin gwamnatin Syria sun yi musayar wuta da 'yan bindigar a cikin harabar asibitin, inda suka kashe wasu daga cikinsu, kuma suka kame wasu kimanin dari da hamsin.
982317