IQNA

An Kai Harin Ta’addanci A Kusa Da Hubbarenn Sayyida Zainab (AS) A Syria

22:12 - April 11, 2012
Lambar Labari: 2303054
Bangaren kasa da kasa, an kai harin ta’addanci a kusa da hubbaren sayyida Zainab (AS) da ke birnin Damascus fadar mulkin kasar Syria lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tare da jikkatar wasu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, an kai harin ta’addanci a kusa da hubbaren sayyida Zainab (AS) da ke birnin Damascus fadar mulkin kasar Syria lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tare da jikkatar wasu wanda kuma hakan ya zo ne a daidai lokacin da ake shirin dakatar da bude wuta.
Wannan harin ta’addanci ya zo ne sakamakon tunzura ‘yan ta’adda da kasashen Amurka da Saudiyya gami da Qatar suke yi kan su ci gaba da kai hare-hare a ko’ina cikin fadin Syria, da nufin kawo cikas ga yunkurin da tsohon sakatare janar na majalisar dinkin duniya yake yi domin ganin an kawo karshen rikicin na kasar Syria cikin gaggawa, lamarin da ya ya tabbata kasashe masu kiyayya da Syria suka shiga cikin rudani.
Kai harin ta’addanci a kusa da hubbaren sayyida Zainab (AS) da ke birnin Damascus fadar mulkin kasar Syria lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tare da jikkatar wasu, wata alama ce ta yunkurin makiya muslunci da al’ummar musulmi na kawo sabani a tsakaninsu, wanda kjasashen Saudiyya da Qatar suke aiwatarwa.
982362


captcha