IQNA

Zanga-Zangar Miliyoyin Mutane Domin Kin Amincewa Da Takarar Sulaiman A Masar

22:31 - April 11, 2012
Lambar Labari: 2303072
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zanga-zangar miliyoyin mutane a kasar Masar a ranar juma’a mai zuwa domin nuna rashin amincewa da takarar mataimakin tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Umar Sulaiman.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shurouk news cewa, an shirin gudanar da zanga-zangar miliyoyin mutane a kasar Masar a ranar juma’a mai zuwa domin nuna rashin amincewa da takarar mataimakin tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Umar Sulaiman wanda Amurka da Isra’ila gami da Saudiyya suke goyon bayansa.
Amma alamu suna nuna cewa Umar Suleiman tankarar majalisar mahukuntan soja ne wanda suke fatar ya sami nasara don kare manufofinsu. Daga waje kuwa sanarwar tsayawa takara da Umar Suleiman ya yi ta sami marhaban lale daga Amurka, Saudiya da Isra'ila kuma wadannan kasashen sun kira shi da cewa mutum ne da ya dace da shugabancin kasar Masar. A daidai lokacin da Umar Sulkeiman ya yi wannnan sanarwa hukumar mulkin sojan kasar Masar da kotun ayyukan gudanarwa sun fara take-taken soke 'yan takarar wasu daga cikin kungiyoyin siyasa.
Bayanai suna nuni da cewa da akwai yiwuwar a soke tsayawar Khairat al-Shadiri dan takarar kungiyar Ikhwan Muslimin wanda ya shiga kurkuku a shekarar 2007 zamanin mulkin Husni Mubarak bisa tuhumar da ta shafi taaddanci. Hakazalika an hana Aiman Nur dan takarar jamiyar Al-Ghad tsayawa saboda gwamnnatin Mubarak ta tsare shi a shekarar 2009.
A karkashin dokokin zaben kasar Masar duk mutumin da kotu ta yanke masa hukuncin dauri ba zai sake samun hakkokinsa na siyasa ba sai bayan shekaru 6 bayan fita daga gidan yari. Hakazalika an soke takarar dan takaran kungiyar Salafiyya Hazim Abu Isma'il domin mahaifiyarsa tana da fasfo na kasar Amurka kuma dokar Masar ta ce dole mahaifan dan takara kada su kasance suna da dan-kasanci na wata kasa ta daban.
Wani abin lura shi ne a jiya 8 ga watan Apirilu ne aka kawo karshen gabatar da takardun tsauyawa takarar zaben na shugaban kasa. Takarar Umar Suleiman dai wacce ta sami goyon bayan Amurka da Israila da Saudiya, bisa dukkan alamu masu kokarin murkushe juyin juya halin alummar Masar sun dauki gagarumin mataki domin cimma burinsu. 982539
captcha