Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Kotu ta yankewa wasu yan kasar Tunusiya Biyu hukumcin zama a gidan yari karkashin leifin da ta same su da shi na cin mutuncin Kur'ani mai girma kuma an yanke masu hukumcin zama a gidan yari na tsawon shekaru hudu a gidan yari da kuma biyan wasu kudade.a zaman kotun na biyu na bin diddigin zargin da ake yiwa Ramzi bin Sa'ad Absha na kaiwa wasu masallatai hudu hari a garin Bankardar tare da cin mutuncin kur'ani mai girma kuma aranar ashirin da uku ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in ne aka yanke masu wannan hukumcin da biyan dinari dari da ashirin.
984502