IQNA

Dubban Dalibai Sun Gudanar Da Gangamin Nuna Goyon Baya Ga Al'ummar Pakistan

18:24 - April 15, 2012
Lambar Labari: 2305364
Bangaren kasa da kasa, dubban daliban addinin muslunci a birnin Najaf na kasar Iraki sun gudanar da wani gagarumin gangami a tsakiyar birnin domin nuna cikakken goyon bayansu ga al'ummar kasar Pakistan musamman mabiya mazhabar iyalan gidan amnzon Allah da ake zalunta.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na NUN cewa, dubban daliban addinin muslunci a birnin Najaf na kasar Iraki sun gudanar da wani gagarumin gangami a tsakiyar birnin domin nuna cikakken goyon bayansu ga al'ummar kasar Pakistan musamman mabiya mazhabar iyalan gidan amnzon Allah da ake zalunta, ta hanyar kai musu hare-hare.

A bangare guda kuma majiyar tsaro a kasar Pakistan ta habarta cewa, sama da mutane 390 suka arce daga wani gidan kaso da ake tsare da su a arewacin, bayan da wasu masu dauke da makamai suka kaddamar da hari kan gidan kason.
Kakakin rundunar 'yan sandan kasar Pakistan Mir Sahib jan ya sheda cewa, da jijjifin safiyar yau ne gungun 'yan bindigar suka kai farmaki kan gidan kason, inda suka yi musayar wuta da jami'an tsaro, sun kuma balle kofofin gidan kaso da rusa wasu bangayensa, lamrin da ya baiwa daruruwan fursunoni damar tserewa, wadanda aka tabbatar da cewa adadinsu ya kai 390.
A nata bangaren kungiyar Taliban a kasar Pakistan ta sanar cewa mayakanta ne suka kai wannan hari, kuma sun tseratar da wasu daga cikin mambobin kungiyar da ake tsare da su, kuma tuni wasunsu har su isa gidajensu.



985032

captcha