Bangaren kasa da kasa: gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi awangaba da wasu masu rajin kare hakkin Palasdinawa su arba'in a daidai lokacin da suke kokarin gabatar da wani shiri mai suna barka da zuwa Palasdini kuma suna kan hanyarsu ta zuwa yankin Palasdinu ne suka kama su a filin sabka da tashin jirage na bin Gurin a birnin Tel Aviv da kuma tsare su.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi awangaba da wasu masu rajin kare hakkin Palasdinawa su arba'in a daidai lokacin da suke kokarin gabatar da wani shiri mai suna barka da zuwa Palasdini kuma suna kan hanyarsu ta zuwa yankin Palasdinu ne suka kama su a filin sabka da tashin jirage na bin Gurin a birnin Tel Aviv da kuma tsare su.A ranar ashirin da bakwai ne ga weatan farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya yan sandan gwamnatin Haramtacciyar kasar isra'ila suka tsare da yin awangaba da wasu yan kasar Faransa su talatin da uku da wasu yan italiya biyu day an Spian biyu da kuma dan kasar Suiziland daya dan kasar Kanada Daya da kumawani daga Portigal dukansu masu gudanar da ayyukan da suka shafi kare hakkin dan adam kuma sun guduri aniyar isa yankin Palasdinu ne domin bayyanawa duniya yadda ake take hakkin al'ummar Palsdinu da kuma yadda ake zaluntarsu a fili babu mai cewa uffin ko yunkurowa domin kubutar das u daga zaluncin Haramtacciyar kasar isra'ila da masu mara mata baya.
986816