IQNA

Zaman Bincike Da Kuma Gyare-Gyare A tarjamar Kur’ani A Yarukan Jamus Da Rasha A Iqna

21:45 - April 18, 2012
Lambar Labari: 2307897
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zama na musamman domin bincike kan tarjamar kur’ani mai tsarki da aka yi a cikin harsunan Jamusanaci da kuma rashanci a baban ofishin yada labaran kur’ani na kasa da kasa da ke jamhuriyar muslunci ta Iran wato Iqna.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, za a gudanar da wani zama na musamman domin bincike kan tarjamar kur’ani mai tsarki da aka yi a cikin harsunan Jamusanaci da kuma rashanci a baban ofishin yada labaran kur’ani na kasa da kasa da ke jamhuriyar muslunci ta Iran wato Iqna da ke birnin Tehran.
Bayanin ya ci gaba da cewa bisa la’akari da muhimamncin da ke tattare da yin sahihiyar tarjama a cikin kur’ani mai tsarki, wannan ya sanya an gayyaci wasu daga cikin masana harsunan da kuma dabinsu, ta yadda hakan zai bayar da damar yin bincike yadda ya kamata, domin tabbatar da cewa tarjamar ta yi daidai da abin da ke cikin kur’ani, ba tare da canja manufa ba.
Wannan kamfanin dillancin labarai dai yana yin matukar kokarinsa domin ganin cewa an tarjama kur’ani mai tsarki zuwa muhimman yaruka na duniya, ta yadda ilmomin kur’ani mai tsarki za su isa ga dukaknin al’ummomi na duniya.

986793


captcha