Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillncin labarn kasar bhrain cewa, an fara gudanar da wani taro na malamai da suke duba wani babban mushafin kur'ani na kasa da aka rubuta a Bahrain wanda kwamitin kula da harkokin kur'ani mai tsarki na kasar ya dauki nauyin shirayawa da gudanarwa a cikin kwaakin nan.
A bagare guda kuma Jami'an tsaron kasar Bahrain sun kame jagororin 'yan adawa sama da 80 a kasar a jiya a lokacin da al'ummar kasar ke gudanar da zanga-zangar neman sauyi ta hnayar lumana, duk kuwa da matakan yin amfani da karfi da mahukuntan kasar suke dauka a kansu.
Rahotanni daga birnin Manama sun tabbatar da cewa, jami'an tsaron sun yi amfani da kulake da harsasai gami gami da hayaki mai sanya hawaye da ke dauke da sanadarai masu guba kan masu zanga-zangar, lamarin da ya yi sanadiyar shakewar lumfani ga daruruwan kanan yara da mata da suke cikin gidajensu gami da dubban masu zanga-zanga.
Jami'an tsaron na masarautar Bahrain sun kame wasu shugabannin kungoyoyin farar hula gami da jami'iyun adawa da suke cikin zanga-zangar, kamar yadda suka bi gida-gida suna kame wasu, lamarin da ya kara tunzura dubban mutane wajen ci gaba da zanga-zangar har tsakar daren jiya.
988559