Bangaren kasa da kasa, za a sanar da sakamakon zaman shari'ar mutumin nan mai cin zarafin musulmi da addinin Musulunci a kasar Tunisia ta hanyar wulakanta abubuwa masu tsarki a cikin wannan addini da yake yi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jeuneafrque cewa, za a sanar da sakamakon zaman shari'ar mutumin nan mai cin zarafin musulmi da addinin Musulunci a kasar Tunisia ta hanyar wulakanta abubuwa masu tsarki a cikin wannan addini da yake yi bisa hujjar bayyana ra'ayi da 'yancin fadar albarkacin baki.
Bayanin ya ci gaba da cewa bayan da kotun birnin Tunis ta gudanar da zaman na shari'a kan shugaban talabijin din Nisma TV, ta sake daga ranar sauraren hukunci na karshe kan wannan shari daga zuwa makonni biyu masu zuwa, inda za a yanke hukunci kan kansa bisa dokoki na kundin tsarin mulkin kasar.
Yanzu haka dai an gudanar da zaman kuma za a sanar da sakamakon zaman shari'ar kan mutumin mai cin zarafin musulmi da addinin Musulunci a kasar Tunisia ta hanyar wulakanta abubuwa masu tsarki a cikin Musulunci, da yin hawan kawara kansu.
989651