IQNA

Al'ummar Masar Sun Fara Nuna Rashin Amincewa Da Salon Mulkin Soji

20:05 - April 21, 2012
Lambar Labari: 2309360
Bangaren kasa da kasa, al'ummar kasar Masar sun fara nuna rashin gamsuwarsu da yadda majalisar mulkin soji ta kasar take gudanar da harkokinta da suke kallo a matsayin wani mulki na kama karya lamarin da ya sanya su sake yin tunanin wani sabon juyi.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi cewa, al'ummar kasar Masar sun fara nuna rashin gamsuwarsu da yadda majalisar mulkin soji ta kasar take gudanar da harkokinta da suke kallo a matsayin wani mulki na kama karya lamarin da ya sanya su sake yin tunanin wani sabon juyi domin kawo karshen mulkin sojoji.

Dan takarar zaben shugaban kasa na kungiyar Ikhwan Muslimin a kasar Masar Khairat al-Shateer ya ce majalisar mulkin sojan kasar ba ta da niyar mika mulki ga farar hula, tashar talbijin ta Press tv ta jiwo al-Shateer yana fadi a jiya Laraba a birnin Alkahira cewa, "A gani na majalisar mulkin soja ba da gaske take ba kan batun mika mulki."

Hakazalika al-Shateer ya zargi majalsar sojin da cewa tana neman mutumin da zata iya juya ta bayan fage ya zama shugaban kasa, AL-Shater ya bayyana soke tsayawarsa takara da hukumar zabe ta yi da cewa alama ce mai nuna cewa za a yi magudi a zaben shugaban kasa na farko bayan faduwar Husni Mubarak.

A nata gefen hukumar zaben ta ce ta soke takarar al-Shater da wasu yan takata 9 ne bisa dokar zaben kasar.

989656



captcha