IQNA

Zanga-Zangar Miliyoyin Mutanen Masar Domin Fayyace Makomar Juyi

20:05 - April 21, 2012
Lambar Labari: 2309361
Bangaren kasa da kasa, miliyoyin mutanen kasar Masar suna gudanar da zanga-zangar neman fayyace makomar juyin juya halin da suka yi wanda ya kawo karshen mulkin kama karya a kasar wanda kuma suke ganin cewa har yanzu dai bat a rinu bat a yi shudi daga yadda lamarin mulkin kasar ke tafiya.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi cewa miliyoyin mutanen kasar Masar suna gudanar da zanga-zangar neman fayyace makomar juyin juya halin da suka yi wanda ya kawo karshen mulkin kama karya a kasar wanda kuma suke ganin cewa har yanzu dai bat a rinu bat a yi shudi daga yadda lamarin mulkin kasar ke tafiya wanda har yanzu kasashe masu girman kai suke da hannu a cikinsa.

A bangare guda kuma a yau ne ake fara sharai'ar mutane 75 da aka kama a kasar Masar dangance da boren da aka yi a filin wasan kollon kafar garin Port Saiid a watan Feburariru, za a saurari shari'ar ne a kotun tafi da gidanka da ke makarantar yan sanda a waje da birnin Alkahira maimakon gudanar da ita a garin na Port Said inda rikiicn ya faru, a wannan kara dai ana tuhumar jamian yan sanda tara da jamian kulob din al-Masri uku, da laifukan da suka hada da kisan kai da kuma sakaci dangane da tsaro.

A ranar 1 ga watan Feburariru ne rikici ya barke a filin wasan kwallon kafa na garin Port Said bayan da aka kammala wasa tsakanin kulob din al-Masry na garin da kuma kulob din al-Ahali na birnin Alkahira, kuma mutane 74 suka rasa rayukansu a sakamakon rikicin.

988860


captcha