IQNA

Masarautar Bahrain Na Yin Ammfani Da Gasar Motoci Domin Murkushe Masu Neman sauyi

22:33 - April 22, 2012
Lambar Labari: 2310226
Bangaren kasa da kasa, gidan sarautar kama karya na Ali-khalifa akasar Bahrain na yin amfani da gasar motocin da ake yia kaar domin murkushe zanga-zangar lumana dakuma nuna ma duniya cewa tamkar kasar ba ta fama da wani bore daga al’ummarta, wanda kuma kasashen yammacin turai ne suke ba shi kariya kan ta’adddancinsa akan faren hula.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alwasat cewa, gidan sarautar kama karya na Ali-khalifa akasar Bahrain na yin amfani da gasar motocin da ake yia kaar domin murkushe zanga-zangar lumana dakuma nuna ma duniya cewa tamkar kasar ba ta fama da wani bore daga al’ummarta, wanda kuma kasashen yammacin turai ne suke ba shi kariya kan ta’adddancinsa a kan faren hula da suke neman hakokinsu da aka haramta musu.
A nasa bangaren dan mulkin kama karya sarkin kasar Bahrein Hamad Ben Issa Al-Khalifa, ya nuna gamsuwarsa da yanda za a fara babbar gasar tsereren motocin nan da ake kira grand prix na formule 1, duk da zanga-zangar da kasar ta ke fama da ita don samar da sauye-sauye a bangaren jagorancin kasar.
Kungiyoyin kare hakkin dan Adam, sun soki yanda za a gudanar da wannan babban wasa alhalin kasar na fama da rikicin cikin gida na siyasa.
Kasar ta Bahrein, na fama da boren al'umma wanda jama'ar kasar mafi rinjiya yan chi'a ke jagoranta don matsa kaimi ga masarautar kasar da tsiraru yan sunna kea kai don a samar da sauye-sauyen siyasa a cikin kasar, jama'ar dake zanga-zangar sun yawaita fitowa a yan kwanakin nan, don nuna adawarsu ga wannan babban wasa, domin a cewarsu ba wasa kasar ke bukata ba a halin yanzu, sai dai a kowane lokaci jami'an tsaro na tarwatsa su da kama wasunsu, yan shi' masu adawa a kasar sun shaida mutuwar wani daga masu zanga-zangar a jiya.
Sarkin, ya nemi ya kwantar da hankalin masu bukatar sauyin, da basu tabbacinsa game da sauye-sauyen da kuma amincewa da batun sulhuntawa a cikin kasar baki daya, tare da cewa kofarsa a bude take don tattamnawan tsakanin yan kasar ta Bahrein. 990042
captcha