IQNA

DalibanJami’a A Bahrain Sun Yi Zanga-Zangar Neman Sakin Khawajah

21:47 - April 24, 2012
Lambar Labari: 2311998
Bangaren kasa da kasa, dubabn daliban jami’a sun gudanar da zanga-zangar neman sakin fitaccen mai kare hakkokindan adan na kasar Abdulhadi Al-khawajah da mahukuntan kasar suke tsare da shi saboda kare hakkokin fararen hula da yake yi daga zluncin da ake yi musu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sdarwa na yanar gizo na presstv cewa, dubabn daliban jami’a sun gudanar da zanga-zangar neman sakin fitaccen mai kare hakkokindan adan na kasar Abdulhadi Al-khawajah da mahukuntan kasar suke tsare da shi saboda kare hakkokin fararen hula da yake yi daga zluncin da ake yi musu daga bangaren mahukuntan ksar.
masarautar kasar Bahrain karakshin mulkin gidan khalifa suna yin abin da haramtatcciyar kasar Isra’ila ma ba ta yi na tsabar zalunci da danne hakkkokin mutanen kasar marassa kariya kamar yadda kuma sauran kasashen dunbiya suke ba ta kariya kan wannan ta’addanci kan fararen hula.
Lauyan Zainab al-Khawajan ne ya sanar da hakan inda ya ce jami'an tsaron sun sako ta bayan kwanaki suna tsare da ita sakamakon shiga cikin zanga-zangar da al'ummar kasar suka shirya don a saki mahaifinta wanda mahukunta suka yanke masa hukumcin daurin rai da rai sakamakon shirya zanga-zangar neman sauyi a kasar da mahukunta suka ce wani kokari ne na kifar da gwamnatin kasar.
Yayin da ya ke magana kan yanayin da Abdulhadi al-Khawajan, wanda yake ci gaba da yajin cin abin na tsawon watanni biyu, Lauyan yace yana cikin mawuyacin hali ainun. 'Yan adawa a kasar Bahrain din dai sun ja kunnen mahukuntan da su guji abin da zai biyo baya matukar dai al-Khawajan ya rasu sakamakon yajin cin abincin da yake yi.
991826


captcha