Bangaren kasa da kasa, daruruwan mutane sun yi zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin kasar saudiyya da ke birnin Alkahira na kasar Masar domin nuna rashin amincewa da abin da kasar ta ke yin a shigar shugula a cikin harkokinsu gami da kame wani lauya mai kare hakkokin 'yan adam na kasar da mahukuntan Saudiyya suka kame shi a lokacin da yake yin Umra.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo nashoroknews cewa, daruruwan mutane sun yi zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin kasar saudiyya da ke birnin Alkahira na kasar Masar domin nuna rashin amincewa da abin da kasar ta ke yin a shigar shugula a cikin harkokinsu gami da kame wani lauya mai kare hakkokin 'yan adam na kasar da mahukuntan Saudiyya suka kame shi a lokacin da yake yin Umra a cikin makon da ya gabata.
Masu zanga-zangar sun yi rera taken yin Allawadai da mahukuntan Saudiyya kan matakan da suka dauka na kulla gaba da al'ummar kasar masar, inda gidan sarautar kasar ke fadi tashin ganin ya kawo cikas ko ta wace ga al'uuamr masar saboda boren da suka yi wa babban aminin Saudiyya da Amurk ada Isra'ila Husni Mubrak, wanda ya kawo karshen mulkin kamansa.
Daruruwan mutane sun yi zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin kasar saudiyya da ke birnin Alkahira na kasar Masar domin nuna rashin amincewa da abin da kasar ta ke yin a shigar shugula a cikin harkokinsu gami da kame wani lauya mai kare hakkokin 'yan adam na kasar da mahukuntan Saudiyya suka kame shi a lokacin da yake yin Umra ba tare da wani dalili ba.
992976