Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar nan mai kula da ayyuka na kur’ani a kasar Lebanon da ke da bababn ofishi a birnin Beirut fadar mulkin kasar ta sanar cewa a halin yanzu tana mayar da hankali wajken gudanar da ayyuka na koyarwa domin tabbatar da cewa an kara yada ilimi a tsakanin matasa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cewa, Ahmad Haji Hussain ya bayyana cewa, babbar cibiyar nan mai kula da ayyuka na kur’ani a kasar Lebanon da ke da bababn ofishi a birnin Beirut fadar mulkin kasar ta sanar cewa a halin yanzu tana mayar da hankali wajken gudanar da ayyuka na koyarwa domin tabbatar da cewa an kara yada ilimi a tsakanin matasa na kasar ta Lebanon.
Daruruwan matasan kasar Rasha sun nuna goyon bayansu ga al’ummar palastinu da suke fuskantar zalunci da danniya daga haramtacciyar kasar Isra’ila a tsawon shekaru ta hanyar mamaye musu yankuna da cin zarafinsu da kame su ba tare da laifin tsaye ko na zaune ba.
Daruruwan matasan sun taru ne a wani babban dandali da ke tsakiyar birnin Moscow na kasar Rasha inda suka daga tutoci na kasashen Rasha da kuma palastinedomin nuna cikakken goyon bayansu ga wannan al’umma da take fuskantar zalunci daga yahudawan sahyuniya, tare da amincewa manyan kasashe na duniya kama su Amurka da Birtaniya gami da Faransa da sauransu.
Rahoton ya ce daruruwan matasan kasar Rasha sun nuna goyon bayansu ga al’ummar palastinu da suke fuskantar zalunci da danniya daga haramtacciyar kasar Isra’ila a tsawon shekaru ta hanyar mamaye musu yankuna da cin zarafinsu da kame su da yin kisan gilla a kansu.
992806