Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi cewa, dubban mutane ne suka taru a jiya Juma a babban dandalin na na birnin Alkahira na Tahrir domin tabbatar wa duniya cewa suna nan daram kan bakansu an kin amincewa da matakin da majalisar sojin kasar ta dauka na kokarin ci gaba da mulki a bayan Husni Mubarak tare da zartar da abubuwan da yake a lokacinsa da ya yi mulkin kama karya.
A karon farko tun bayan faduwar gwamnatin kama karya ta Husni Mubarak a kasar Masar; Dubban al'ummar Masar sun fito fili a sassa daban daban na kasar suna gudanar da zanga zangar yin Allah wadai da haramtacciyar kasar Isra'ila, tare da neman yin watsi da yarjejeniyar zalunci ta Camp David da aka kulla tsakanin kasar Masar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.
A yankin Arish da ke kudancin kasar Masar dubban al'ummar yankin ne suka fito suna zanga zangar yin Allah wadai da haramtacciyar kasar Isra'ila, tare da rera taken neman yin watsi da yarjejeniyar zalunci ta Camp David.
Yarjejeniyar Camp David dai yarjejeniya ce ta sulhu da zaman lafiya da aka kulla tsakanin kasar Masar da haramtacciyar kasar Isra'ila tun a shekara ta 1978 a sansanin Camp David na kasar Amurka. Camp David sunan waje ne da aka kebance wa manyan jami'an kasar Amurka da iyalansu domin shakatawa, don haka yarjejeniyoyi biyu da aka kulla a wannan wajen tsakanin kasar Masar da haramtacciyar kasar Isra'ila a ranar 17 ga watan Satumban shekara ta 1978, da kuma wadda aka kulla tsakanin hukumar cin gashin kan Palasdinawa da h.k.ta Isra'ila a ranar 11 ga watan Yulin shekara ta 2000 suka shahara da sunayen yarjejeniyoyin Camp David.
Tun bayan kulla yarjejeniyar Camp David tsakanin kasar Masar da haramtacciyar kasar Isra'ila; al'ummar Masar suke adawa da wannan yarjejeniyar, tare da daukarta a matsayin yarjejeniya maras halacci, kuma a sakamakon haka ne wasu tawagar sojojin Masar masu kishin kasa karkashin jagorancin Khalid Islambuli suka halaka shugaban kasar ta Masar Anwar Sadat da ya rattaba hannu kan yarjejeniyar ta Camp David.
Daga cikin manyan illolin da yarjejeniyar Camp David ta kunsa akwai batun Masar zata sayarwa haramtacciyar kasar Isra'ila da iskar gas a farashi mai rahusa, lamarin da al'ummar Masar ke daukansa a matsayin wulakanta arzikin kasa, baya ga mika kai ga munanan manufofin yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida da hakan ya mai da kasar ta Masar a matsayin 'yar koran h.k.Isra'ila, lamarin da ya tilastawa kasashen Larabawa a wancan lokacin yanke alakar jakadanci da kasar Masar.
Yau tsawon shekaru 33 da kulla yarjejeniyar Camp David amma har yanzu al'ummar Masar suna nan a kan azamarsu ta kiyayya da yarjejeniyar, kuma a bayan gagarumar nasarar hambarar da gwamnatin kama karya ta Husni Mubarak; al'ummar Masar sun nemi kawo karshen alaka tsakanin kasarsu da haramtacciyar kasar Isra'ila, tare da jaddada goyon bayansu ga al'ummar Palasdinu da yahudawan sahayoniyya ke zalunta.
A halin yanzu haka dai ra'ayin da ke watsuwa tsakanin 'yan siyasar kasar Masar dangane da yarjejeniyar Camp David shi ne: Wasu na ganin a canja sigar yarjejeniyar ta hanyar yi mata gyarar fuska, wasu na ganin a yi watsi da yarjejeniyar kwata- kwata, yayin da wasu ke da ra'ayin bada dama ga al'ummar Masar su bayyana matsayinsu kan yarjejeniyar ta hanyar gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a.
994308