Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijindin Almanar cewa, kungiyar gwagwarmayar msul;unci ta hizbulahh ta yi kakausar suka da yin Allawadai da harin bam din da aka kai a kan babban ofishin jam'iyyar Al-tauhid a birnin Beirut fadar mulkin kasar ta Lebanon da ke yankin bak'ata da ke cikin birnin.
A Wani rahoton kuma Jami'an tsaron kasar Lebanon sun sanar da kame wani babban jirgin ruwa da ya fito daga kasar Libya shakare da makamai da sanadaran hada bama-bamai, wanda za a kai su ga 'yan tawayen kasar Syria.
Mai aiko ma gidan talabijin din Al-alam rahotanni daga birnin Beirut na kasar Lebanon ya habarta cewa, jami'an tsaron kasar Lenabon da suke sintiri a cikin ruwa sun tare jirgin ruwan wanda ya fito daga kasar Libya, bayan da suka bincika shi, sun samu tarin makamai, da suka hada da manyan bindigogi, da makaman RPG da sanadaran hada makamai, kuma an nufin mika su ne ga 'yan tawayen Syria.
Tun kafin wannan lokacin da gwamnatin Syria ta tabbatar da cewa, mafi yawan makaman da 'yan ta'addan kasar suke yin amfani da su wajen kai hare-hare a cikin kasar, ana shigo da su ne ta iyakokin kasar da kuma kasar Lebanon.
994518