IQNA

Kungiyoyin Kare Hakkin Bil Adama Sun Soki Saudiyya Kan Cin Zarafin ‘yan Adam

23:01 - April 29, 2012
Lambar Labari: 2314675
Bangaren kasa da kasa, kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasashen duniya sun yi kakausar suka dangane da cin zarafin bil adama da ake yi a kasar Saudiyya musamman am a cikin lokutanna nan mutanen kasar suke mikewa suna neman hakkokinsu da aka haramta musu.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, uya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Alhad TV cewa, kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasashen duniya sun yi kakausar suka dangane da cin zarafin bil adama da ake yi a kasar Saudiyya musamman am a cikin lokutanna nan mutanen kasar suke mikewa suna neman hakkokinsu da aka haramta musu, bugu da kari da irin matakan da mahukuntan kasar suke dauka na taimaka ma masarautar Bahrain domin murkushe fararen hula masu zanga-zangar lumana.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa "Amnesty International "ta bukaci a gudanar da bincike akan kisan da jami'an tsaro su ka yi wa wani mai zanga-zanga a gabacin saudiyya, a wani bayani da kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta fitar ta bukaci a yi bincike mai zaman kanshi akan kisan da aka yi wa Isam Muhammad Abu Abdullah a lokacin da ya ke cikin zanga-zanga a garin Awamiyyah da ke gabacin Saudiyya.
Bayanin kungiyar ya ci gaba da cewa: "Zanga-zangar ranar alhamis din da ta gabata an yi ta ne domin kira da a saki fursunonin siyasa da ake tsare da su da kuma kawo karshen wariyar da ake yi wa 'yan shi'a a yankin, a cikin watannin bayan nan dai jami'an tsaron Saudiyya sun rika bude wuta akan masu zanga-zangar lumana da su ke son a samar sa sauye-sauye na siyasa a cikin kasar.
994635
captcha