Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Birgediya Janar Mas’ud Jaza’izi mataimakin babban hafsan dakarun kare juyin juya halin muslunci a jamhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa kasantuwar sojojin kasashen ketare a cikin yankin gabas ta tsakiya shi ne babban abin da ya jawo matsala da rashin zaman lafiya a yankin baki daya.
Sheikh Hasdsan Saffar daya daga cikin malaman addinin muslunci a yankin Katif da ke gabacin kasar Saudiyya ya kirayi ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar da ta gudanar da bincike a cibiyoyin addini na mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah idan har tana shakku kan kasantuwarsu ‘yan kasa kamar yadda ake rayawa.
A ci gaba da murkuhe duk wani yunkuri na neman hakkokin su da suke a yankin gabacin Saudiya a nasa bangaren jami'an tsaron Saudiyya sun bude wutan bindiga kan masu zanga zangar lumana lamarin da ya yi sanadiyyar shahadar mutum guda tare da jikkata wasu da dama a garin Awamiyya da ke gabashin kasar.
A jiya juma'a ne daruruwan al'ummar garin Awamiyya da ke gabashin kasar Saudiyya suka gudanar da zanga zangar lumana mai taken "Fushin 'Yantattu" domin nuna fushinsu kan kashe Munir Midani tare da jikkata wasu 14 na daban a ranar alhamis da ta gabata, suna rera taken neman kawo karshen mulkin kama karya na gidan sarautan Ali-Sa'ud da sakin dukkanin fursunonin siyasa da ke gidajen kurkuku da kuma wanzar da 'yanci ga al'ummar kasar, don haka jami'an tsaron kasar suka bude musu wuta lamarin da ya janyo shahadar wani matashi mai suna Zuhair Abdullahi da kuma jikkata wasu da dama.
Har ila yau al'ummar garin Kadif da ke yankin gabashin Saudiyya sun gudanar da zanga zangar lumana suna kiran da a aiwatar da hukuncin kisa kan jami'an tsaron kasar da suka bude wuta kan masu zanga zangar lumana da neman sakin fursunonin siyasa tare da jaddada aniyarsu ta ci gaba da gudanar da zanga zangar har sai sun kai ga bukatunsu.
995888