Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al'adu da ilimi cewa, tsananin adawar da ake yi da addini muslunci a cikin kasashen turawa shi ne babban dalilin da yasa ake samun mutane masu kekasassar zuciya da rashin ‘yan adamtaka da suke kone kur’ani mai tsarki wanda hakan ya ke ci gaba da yaduwa a cikin kasashensu kamar dai yadda duniya take shedawa a halin yanzu.
Yanzu haka ana shirin gudanar da wata gagarumar zanga-zangar nuna cikakken goyon bay aga al’ummar palastinu a gaban ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya domin tabbatar wa duniya cewa masu lamiri a cikin mutane ako’in acikin duniya ba su goyon bayan abin da ake yi a kana fararen hula palastinawa.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gangamin dai babbar cibiyar palastinawan Birtaniya ce ta shirya shi, kuma zai samu halartar wakilan cibiyoyin fararen hula da kuma kungiyoyi na addini, gami da lauyoyi da kuma masu kare hakkokin bil adama da suke da cibiyoyi a birnin London da ma wasu sassa na kasar.
Shirin gudanar da gagarumar zanga-zangar nuna cikakken goyon baya ga al’ummar palastinu a gaban ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke birnin London fadar mulkin kasar Birtaniya wata babbar manuniya ce ta yunkurin al’ummomin duniya da kuma farkawarsu kan babakeren yahudawan sahyuniya.
997975