IQNA

Daruruwan masu Zanga-Zanga Sun Kone Tutocin Amurka Da Isra'ila a Kasar Jordan

13:33 - May 06, 2012
Lambar Labari: 2319461
Bangaren kasa da kasa, daruruwan mutanen kasar Jordan sun gudanar da wata gagarumar zangazanga domin nuna kin amincewarsu da salon siyasar Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila a kan kasashen musulmi da na larabawa, inda suka kone totocinsu a bainar jama'a suna rera taken la'antarsu.
Kamfanin dillnacin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Liwa'a ta kasar Jordan cewa, daruruwan mutanen kasar Jordan sun gudanar da wata gagarumar zangazanga domin nuna kin amincewarsu da salon siyasar Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila a kan kasashen musulmi da na larabawa, inda suka kone totocinsu a bainar jama'a suna rera taken la'antarsu da kuma yin Allawadai da siyasarsu.
Shugabar jam'iyyar Labour a haramtacciyar kasar Isra'ila Chiley Yasimovitch ta suke pira ministan Benjamin Natanyaho kan abin da ta kira babbar kuren da yake tafkawa wajen mayar da kasar Iran ta zama ita ce babbar matsala ga haramtacciyar kasar.
A wata zantawa ta musamman da gidan talabijin a birnin Tel aviv, Chiley Yasimovitch ta bayyana cewa Natanyaho ya mayar da hankalinsa baki daya kan batun shirin nukilyar kasar Iran, tare da yin barazanar kaddamar da harin soji kan tashoshin nukiliyar Iran ko da kuwa Amurka ba ta amince masa da yin hakan ba, alhali kuwa a cewarta wannan babban kure ne.
A ranar 14 ga watan Afirilun da ya gabata ne manyan kasashe 5 gami da Jamus suka koma kan teburin tattaunawa tare da Iran kan shirinta na makamashin nukiliya a birnin Istanbul, kuma za su ci gaba da wannan tattaunawa a ranar 23 ga wannan wata na Mayu. A cikin makon da ya gabata ne wasu jami'an leken asiri a kasar Amurka suka gabatar da bayanin da ke cewa Iran ba ta da wani shiri n kera makaman nukilya, lamarn da ya bakanta wa Benjamin Natanyaho rai matuka.


1000133
captcha