Bangaren kasa da kasa;Masimo Dalima tsohon firaministan kasar Italiya a ranar sha biyar ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya a wani jawabi day a gabatar ga gwamnatocin nahiyar Turai ya bukace su das u bude kofar tattaunawa da fahimtar juna a tsakaninsu da duniyar musulmi da kuma su maida hanka da himma a wannan bangare.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Masimo Dalima tsohon firaministan kasar Italiya a ranar sha biyar ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya a wani jawabi day a gabatar ga gwamnatocin nahiyar Turai ya bukace su das u bude kofar tattaunawa da fahimtar juna a tsakaninsu da duniyar musulmi da kuma su maida hanka da himma a wannan bangare. Tsohon firaministan na kasar Italiya dai ya jaddada cewa a yau akwai muhimmanci matuka gaya a tattaunawa a tsakanin kasashen musulmi musamman idan aka yi la'akari da abubuwan da ke faruwa a yan watannin a yankuna daban daban na duniya musamman yankin Turai da hakan ke bukatar shinfida wata hanya da yanayi na tattaunawa da duniyar musulmi da kuma musulmi da shugabannin addini a daidai wannan lokaci. Har ila yau ya kara da cewa gudanar da irin wannan tattaunawa zai taimaka matuka gaya a bangarori daban daban na siyasa da zamantakewa dafahimtar juna da addini da kuma al'adu da kuma kowa ne zai cimma moriyar hakan.
1000241